Sai an cire ka! Sanatoci sun fadawa Babachir Lawal

Sai an cire ka! Sanatoci sun fadawa Babachir Lawal

Sanatocin tarayyar Najeriya sun ce lallai fa sai sakataren gwamnatin tarayya Mr. Babachir Lawal yayi murabus bisa ga laifuffukan cin hanci da rashawa.

Sai an cire ka! Sanatoci sun fadawa Babachir Lawal

Sai an cire ka! Sanatoci sun fadawa Babachir Lawal

Kwamitin bincike na majalisar dattawan Najeriya sun tuhumeshi ne da laifin rashawa akan kwangilan tallafin yankin arewa maso gabas na biliyoyin nairori.

Yayinda yake Magana da jaridar DailySUn, kakakin majalisar dattawa, Abdullahi Sabi,da shugabn kwamitin man fetur, Sanata Kabiru Marafa, Sanata Peter Nwaboshi sun hada baki sunce wajibi ne yayi murabus ko kuma a cire shi.

KU KARANTA: Obama ya sa kafar wando daya da Trump

Sabi yace: “ Kafofin yada labarai sun fara zama makiyan Najeriya. Suna son tayar da kura akoda yaushe. Ba zan amsa tambayoyin bag aba daya. Kafofin yada labarai bas u kyautawa majalisar dattawa. Shin ba zasu iya aikinsu ba tare bata mana suna bane?"

Sanata Nwaboshi yace tunda wannan abu ya yadu kowa yaji, babu bukatansa yayi wani Magana kuma.

“Na amince da duk abinda majalisar dattawa tace akan zance SGF. Ni ba mamban kwamitin bane. Yan Najeriya su kammala zancesu akan abinda mukayi. Maganan ta zama na kowa da kowa."

Shi kuma Sanata Marafa yace: Wanna wani zance ne wanda mun gana tattaunawa kuma babu abinda zan kara akai. A taron mu na ranan Talata, mun amince cewa kakakin majalisar dattatwa zaiyi Magana da yan jarida kuma ya bayyana musu abin da muka yanke. Ba zan so inyi Magana sabanin abinda muka amaince da shi ba.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel