Sifeto janar na kasa ya nada CSP Moshood sabon Kaakakin hukumar

Sifeto janar na kasa ya nada CSP Moshood sabon Kaakakin hukumar

Babban sufeton yansandan Najeriya Ibrahim Idris ya amince da nada CSP Jimoh Moshood a matsayin sabon mai Magana da yawun hukumar yansandan kasar nan.

Sifeto janar na kasa ya nada CSP Moshood sabon Kaakakin hukumar

Cikin wata sanarwa daga ofishin mai kula da shugabanci na hukumar SP Benjamin Achegbani yace Moshood ya karbi ragamar aiki daga CP Don Awunah wanda ya samu Karin girma zuwa mukamin kwamishinan yansanda a jihar Akwa Ibom.

KU KARANTA: Dan Biafara ya sha wuya a hannun yansanda, yace yana son Buhari

CSP Moshood dan asalin jihar Kwara ne, kuma yana da digiri a fannin kimiyyar siyasa daga jami’ar Ahmade Bello, dake Zaria jihar Kaduna.

CSP Moshood ya taba zama Kaakakin rundunar yansandan babban birnin tarayya Abuja, kuma taba zama DPO a ofishin yansanda dake cikin garin Abuja a tsakankanin shekarun 2012 zuwa 2013.

Bugu da kari Jimoh Moshood ya taba rike sashin kula da kudade da mulki na rudunar yansandan babban birnin tarayya, Abuja, a baya bayan nan ma shike rike da mukamin mataimakin Kaakakin rundunar hukumar yansanda, inda daga nan ne ya samu Karin girma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel