Kogin jihar Binuwe yayi awon gaba da kananan yara guda biyu

Kogin jihar Binuwe yayi awon gaba da kananan yara guda biyu

Wasu yara biyu da suka je yin wankan rafi a kogin jihar Binuwe sun rasa rayukansu yayin da tsumagiyar Kogin tayi awon gaba dasu.

Kogin jihar Binuwe yayi awon gaba da kananan yara guda biyu

Kogin jihar Binuwe

Wani shedan gani da ido ya bayyana cewar yaran da suka hada da dan shekaru 10 da mai shekara 15 sun yi linkaya ne mai zurfi a cikin kogin ta sashin Arewacin gabar kogin, daga nan ne kuma aka rasa inda suka shige sama ko kasa.

KU KARANTA: Za’a sha biki, Messi zai auri budurwasa Antonella

Shaidan gani da idon mai suna Emeka da fari yara Uku ne suka shiga iyo cikin wannan kogi, kuma ruwan yayi tafiya da dukkansu, amma jama’a sun ceto mutum daya daga cikinsu, yayin da sai dai gawar sauran biyun aka tsinta bayan an kwashe awanni 24 ana nemansu.

Zuwa yanzu dai dangin daya daga cikin yaran sun gane dansu, kuma har sun mai jana’iza, yayin da har yanzu ba’a gano yan’uwan dayan mamacin ba.

Sai dai da muka tuntubi Kaakakin yansandan jihar Binuwe Moses Yamu game da batun, sai ya kada baki yace ba shi da masaniya saboda har zuwa yanzu basu samu rahoton faruwar hatsarin ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel