Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

- Hukumar hana fasa kwari na Najeriya wato Kwastam sun cafke sababbin bindigogi 611 da aka boye a kwalaye cikin babban mota a jihar Lagas

- Koda dai hukumar Kwastam bata bayyana daga inda makaman ya fito ko inda yake shirin zuwa ba, akwai rahotanni a wasu bariki cewa makaman sun fito ne daga kasar Sin (China)

- Kwanturola-Janar na hukumar kwastam Hameed Ali ya sanar da kamun wasu mutane uku da ake zargin suna da alaka da shigo da makaman kuma yasa ayi bincike cikin al’amarin

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Hukumar hana fasa kwari na Najeriya wato Kwastam tayi bayanin yadda cafke wasu sababbin makamai guda 661 a jihar Lagas.

A wata sanarwa da Kwamturola-Janar na hukumar NCS Hameed Ali da yake magana a Lagas a ranar Litinin, 30 ga watan Janairu, yace an dakatar da bindigogin a ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu.

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Sababbin bindigogin da aka kama cikin kwalaye

Hukumar Kwastam sun bayyana cewa shigo da makaman yayi karo da dokar Najeriya kuma hakan na raunata matakan tsaro a kasar a halin yanzu.

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Hukumar kwastam din ta cafke bindigogi 661

Hukumar ta Kwastam ta tabbatar da kamun mutane uku dake da alaka da shigo da maggan makaman. An bayyana sunayen su a matsayin: Oscan Okafor (mai shigo da makaman) shekaru 51, Mahmud Hassan (jami’in karban kaya) shekaru 56 da kuma Sadique Mustapha (wanda zai raka kayan zuwa inda za’a kai) shekaru 28.

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: Hukumar Kwastam ta cafke sababbin bindigogi 661 a jihar Lagas (HOTO)

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Bincike ya nuna cewa ba'a taba amfani da bindigogin ba

Hameed Ali yace akwai yiwuwar kama wasu da dama kamar yadda aka bude shafin bincike a cikin al’amarin.

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke a jihar Lagas (HOTUNA)

Hukumar Kwastam sun kama mutane 3 kan bindigogi 661 da aka cafke

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel