To fa! Yan rakiyar amarya 47 sun mutu a hadarin mota

To fa! Yan rakiyar amarya 47 sun mutu a hadarin mota

- Yansanda a kasar Madagascar sun ce yan daukar amarya 47 ne suka mutu lokacin da motar da suke ciki ta fada wani kogi

- Bayanai sun ce an samu hadarin ne kusa da garin Anjozorobe da ke da nisan kilomita 90 daga birnin Antananarivo, kuma cikin wadanda suka mutu har da yara 10

To fa! Yan rakiyar amarya 47 sun mutu a hadarin mota

To fa! Yan rakiyar amarya 47 sun mutu a hadarin mota

Kakakin yan sandan Herilala Andrianatisaona ya ce hadari ya ritsa da angon da amaryar sa.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya caccaki Shugaba Donald Trump kan matakin da ya dauka na hana Musulmi 'yan wasu kasashe shiga kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun Obama, Kevin Lewis, ya fitar ta ce tsohon shugaban ya ji dadin zanga-zangar da ake yi domin tilasta wa Trump ya janye matakin da ya dauka.

Ya kara da cewa Mr Obama yana kyamar nunawa mutane wariya saboda addininsu.

A cewarsa, zanga-zangar da mutane ke yi ta nuna cewa Amurkawa ba za su bari a gurbata mulkin dimokradiyya ba.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da wasu kafafen watsa labaran Amurka suka ruwaito cewa wasu jakadun kasar a kasashen duniya na shirin caccakar Shugaba Donald Trump a kan takaita dokokin karbar bakin-haure.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel