Dan Biafara ya sha wuya a hannun yansanda, yace yana son Buhari

Dan Biafara ya sha wuya a hannun yansanda, yace yana son Buhari

Wani mai karajin samar da kasar Biafra kuma mawallafin jaridar Biafara yayi ma shugaba Buhari magiya daya yi mai afuwa bayan ya shiga hannun hukumar yansanda a ranar Litinin 10 ga watan Janairu, inda ya bayyana musu shifa bashi da nufin ganin Najeriya ta tarwatse.

Dan Biafara ya sha wuya a hannun yansanda, yace yana son Buhari

Mawallafin Jaridar ta Biafara yace: “Ina kaunar Najeriya, kuma ina kaunar shugaba Buhari,, bani da nufin yakar kasata, manufata kawai in sadar da jama’a da labarai, musamman wadanda basu da damar shiga yanar gizo.

KU KARANTA: Uwargidar ministan shugaba Buhari ta rasu

“A lokutta da daman a kan samo labarai ne daga yanar gizo, wadanda nake bugawa ina sanar da mutane, a yanzu haka inda labaran dana buga akan wasanni da zamantakewa.”

Mawallafin na jaridar Biafara, wanda aka sakaya sunansa saboda dalilin tsaro ya amsa cewar kimanin shekaru 8 ya kwashe yana harkar buga jarida, amma watanni 2 da suka gabata ne ya fara buga jaridar Biafara Times, kamar yadda yace, ya fuskanci jama’ar kudu maso gabas, inyamurai kenan suna saye jaridun nasa gaba daya

“Muna buga kwafi 5000 ne, kuma siyar da kowane kwafi kan N100.”

Kwamishinan yansandan jihar Legas, Fatai Owoseni yace sun kwato kwafi 515 na jaridar Biafara Times yayin samamen da suka kai a ofishin jaridar dake unguwar Shomolu, jihar Legas.

“Mun garkame ofishin buga jaridar, sa’annan muna sa ido akan sa. Wannan babban laifi ne a karkashen dokar manyan laifuka na jihar Legas.” Inji Kwamishinan.

Ana samun mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel