Da alamu Gwamnan Kaduna bai zo da wasa ba

Da alamu Gwamnan Kaduna bai zo da wasa ba

– Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya nuna ba da wasa yake ba

– Gwamnan yace duk Kwamishinan da ba zai iya ba, ya sauka

– El-Rufa’i ya shirya kammala duk wasu manyan ayyuka a wannan shekarar

Da alamu Gwamnan Kaduna bai zo da wasa ba

Da alamu Gwamnan Kaduna bai zo da wasa ba

Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya nuna ba fa wasa ya fito yi ba. Gwamnan yayi kira ga mukarraban sa yace duk wanda ba zai iya ba ya ba shi wuri. Gwamnan yayi wannan jawabi ne a zaman da Gwamnatin Jihar tayi na dabbaga ayyukan wannan shekarar.

Mai Girma Gwamnan ya sha alwashin kammala duk wasu manyan ayyuka da ya dauko a wannan shekarar, ya bayyyana haka ne a wannan taron da Gwamnatin Jihar da Ma’aikatar kasafin kudi su ka hada na kwanaki 2 a jere. Gwamnan ya duba ayyuka da kuren da suka yi a shekarar da ta wuce da niyyar a gyara su wannan shekara.

KU KARANTA: Matar wani Minista ta rasu

Gwamna El-Rufa’i yace daga yanzu dole kowace Ma’aikata ta rika kirkiro manyan ayyukan gina Jiha, ya kuma bada umarni kowane Kwamishina ya rika fita yana duba ayyukan da Jiha ta ke yi. Gwamnan yace daga yanzu zama cikin Ofis ya karewa Kwamishinoni.

Malam Nasiru dai yace duk Ma’aikatar da ba ta kawo kudi, ba za ta ga kudi ba a kwaryar ta. Don haka ne ma Gwamnan yace duk Kwamishinan da ba zai iya tatso akalla Miliyan 10 a wata ba ya tafi gida. Gwamnatin dai tana da kwanaki kusan 850 ta cika alkawuran da ta dauka.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook https://www.facebook.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis
NAIJ.com
Mailfire view pixel