Faston da yayi kira a kashe Fulani ya bayyana hannun DSS

Faston da yayi kira a kashe Fulani ya bayyana hannun DSS

– Cikin kwanakin baya wani Fasto Johnson Suleiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Makiyaya Fulani

– Faston ya gurfana gaban Hukumar DSS

– Fasto Sulaiman yace hakan da aka yi yayi masa daidai

Faston da yayi kira a kashe Fulani ya bayyana hannun DSS

Faston da yayi kira a kashe Fulani ya bayyana hannun DSS

Idan ba a manta ba Babban Limamin cocin nan na Omega Fire, Fasto Johnson Sulaiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Fulani a duk inda suka ci karo da su kusa da cocin sa. Yanzu haka dai Hukumar DSS ta gayyaci Faston, ya kuma amsa gayyatar.

Wannan dai ta sa Hukumar DSS tayi kokarin cafke Faston, ko da hakan ya ci tura, sai aka aika masa goron gayyata. A jiya ne dai Faston ya kama hanya zuwa Ofishin Hukumar, inda muka samu labari zai tafi da Lauyoyi kusan 30. Hukumar CAN dai tace ba za ta rakiyar Faston ba.

KU KARANTA: DSS ta gayyaci Fasto Sulaiman shan shayi

Kafin ya tafi, Faston dai ya kira mabiyan sa da su guji yin zanga-zanga a dalilin kiran na sa da Hukumar DSS tayi. Faston ya nemi mabiyan sa su cigaba da yi wa Najeriya addu’a. Yanzu haka dai har wannan Fasto ya fito bayan ya sha tambayoyi. Faston yace abin da aka yi masa yayi daidai.

Sai dai ba mu san ko me suka tattauna da Hukumar ba. A baya dai Faston yayi huduba a yanka wuyn duk wani Fulani da aka gami ko da wasa kusa da Cocin sa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel