Fayose zai gyara mana PDP, inji wani dan majalisa

Fayose zai gyara mana PDP, inji wani dan majalisa

– Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti ne aka dorawa nauyin gyara Jam’iyyar PDP

– Wani Dan Majalisa ya kira Gwamnan ya kawo karshen rikicin da ke cikin Jam’iyyar

– Honarabul Akande yace duk nan da wata biyu PDP za ta dawo daidai

Fayose zai gyara mana PDP, Inji wani Dan Majalisa

Fayose zai gyara mana PDP, Inji wani Dan Majalisa

Wani Dan Majalisar Jihar Legas Honarabul Victor Akande yace akwai babban aiki a wuyan Gwamna Ayo Fayose wanda aka nada Shugaban Gwamnonin PDP na Kasa. Dan Majalisar yayi kira ga Gwamnan ya sasanta duk rikicin da ke cikin Jam’iyyar.

Victor Akande yace idan har ta kama mai girma Gwamnan ya tsuguna ya roki kowa domin a sasanta ne zai yi hakan. Honarabul Akande yace nan da zuwa Watan Maris za a kawo karshen duk rikicin da ake ta bugawa a Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Babachir: SERAP ta gargadi Buhari

Jaridar Vanguard tace Dan Majalisar yayi kira ga ‘Yan PDP da su ajiye makamin su domin a fahimci juna. Ciki dai wanda Gwamnan yake fada da su akwai irin su Bode George da Sanata Kashamu, Dan Majalisar yace ya dace duk a sasanta domin a tsira tare.

Makon nan ne Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose yace Shugaba Buhari ya jefa Kasar nan cikin wani irin hali. Fayose yace dama ya gargadi mutane game da Buhari, ga shi yanzu babu wanda ya tsira a Kasar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel