Inyamuri na iya shugabancin Kasar nan a 2023 - Gwamna Okorocha

Inyamuri na iya shugabancin Kasar nan a 2023 - Gwamna Okorocha

– Gwamnan Jihar Imo yace tabbas zuwa 2023 Inyamuri zai iya karbar mulki

– Rochas Okorocha yace hakan zai fi sauki idan har Buhari ya kammala wa’adin sa

– Rochas Okorocha yace bai yarda da tsarin ci-ka-bani ba

Inyamuri na iya shugabancin Kasar nan a 2023-Gwamna Okorocha

Inyamuri na iya shugabancin Kasar nan a 2023-Gwamna Okorocha

Gwamnan Jihar Imo, Rochas O. Okorocha ya bayyana cewa Inyamurai su manta da karbar shugabancin Kasar nan a zabe mai zuwa. Gwamna Okorocha yace in dai 2019 ake magana to Inyamurai su cire ran su.

Mai girma Gwamna Okorocha yace zai fi sauki Inyamuri ya karbi mulkin Kasar nan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin sa don haka yayi kira su mara masa baya kurum.

KU KARANTA: Bukola na neman APC ta wargaje?

Gwamnan Jihar Imo yayi wannan jawabi ne kamar yadda Jaridar Cable tace bayan Gwamnan ya gana da Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo a jiya. Rochas Okorocha yace ‘Yan kabilar sa na Inyamurai sun yi karfi a Jam’iyyar APC.

Kwanaki dai mai girma Gwamnan na Jihar Imo ya kira Jama’an sa da su shiga Jam’iyyar APC. Gwamnan yace APC ce kadai jirgin tsira ga Inyamurai a Najeriya. Gwamna Okorocha yace Mutanen Ibo babu abin da ya dace da su irin su shigo tafiyar APC mai mulkin Kasar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel