An bankado wani laifin su Saraki da Dogara

An bankado wani laifin su Saraki da Dogara

– Ta kwabe da Shugabannin Majalisar Kasar nan a halin yanzu

– Wata Kungiya ta bankado barnar da su Saraki suka yi

– Ana zargin Bukola Saraki da Yakubu Dogara da Mataimakan sa da yin sama da wasu Miliyan 600

An bankado wani laifin su Saraki da Dogara

An bankado wani laifin su Saraki da Dogara

Ana zargin Shugabannin Majalisar Kasar nan da yin gaba da wasu kudi sama da Naira Miliyan 600. Kamar dai yadda Sahara Reporters ta fada akwai hannun shi Bukola Saraki da Mataimakin sa; Ike Ekeremadu da kuma Yakubu Dogara da na sa Mataimakin; Yusuf Lasun.

Wata Kungiya mai suna CATBAN ce ta zargi Shugabannin Majalisar Dattawa da Wakilan Tarayyar Kasar da matsawa Hukumar FCDA mai kula da harkokin Birnin-Tarayya Abuja har sai da aka ba su gidajen kwana bayan kuma Gwamnati ta basu kudin gida.

KU KARANTA: Saraki na nema a gyara tattalin arziki

Hukumar ta FCDA mai kula da cigaban Birnin-Tarayyar tace dai ta kashe kudi har N630,125, 499.90 domin kamawa manyan ‘Yan Majalisar haya da kuma gyaran gidajen da aka kaman. Sai dai ashe ‘Yan Majalisun suna zaune cikin gidajen su na kan su ne, sai suka karkatar da kudin da aka ware na hayan su saka a aljihu.

Jiya da aka yi hira da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki yace shi yanzu babban burin sa, tattalin arzikin Najeriya ya dawo daidai.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel