Hotunan Buhari na ci gaba da ta da kura

Hotunan Buhari na ci gaba da ta da kura

- Wasu 'yan Najeriya sun yi kira ga masu taimakawa shugaban kasa da su gabatar da Muhammadu Buhari yayin da ake rade-radi game da lafiyarsa.

-Mun gaji da hada hotuna, ku gabatar mana da Buhari yanzu-yanzu - a gargadin da aka yi wa fadar shugaban kasa.

Hotunan Buhari na ci gaba da ta da kura

Hotunan Buhari na ci gaba da ta da kura

Shugaba Muhammadu Buhari ya bar Abuja ranar Alhamis 19 ga watan Janairu don neman lafiya a kasar Ingila inda zai samu kulawa a cikin hutunsa na shekara na kwana 10.

Amma tun lokacin da shugaban ya yi balaguro, wani bangare na kafafen yada labarai ke yada jita-jita game da matsayin lafiyar tasa, inda wasu rahotannin ke cewa ya mutu a Landan.

Amma kuma, fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahoton a inda ta ce ba gaskiya ba ne, ta kuma fitar da hotunan shugaban a can birnin Landan inda ya ke hutawa.

Wani hoton na Buhari da uwar gidansa ya fito don ya tabbatar da cewa shugaban kasa na nan da ransa kuma cikin koshin lafiya.

Wani sabon hoto da fadar ta fitar ya na nuna Buhari su na cin abinci da gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun a Landan ranar Litinin 30 ga watan Janairu ya kara haifar da kiraye-kiraye cewa shugaban ya yi wa 'yan Najeriya magana don warware jita-jitar da ake yadawa game da lafiyarsa.

Wasu 'yan Najeriya da su ka yi magana game da sabon hoton sun yi zargin cewa hoton hadi ne kawai, su na masu bukatar hoton bidiyo don gasgata abin da fadar shugaban ta yi ikirari na cewa Buhari na cikin koshin lafiya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel