Ni ban damu dan a kafa sabuwar Jam’iyya ba, Inji Saraki

Ni ban damu dan a kafa sabuwar Jam’iyya ba, Inji Saraki

– Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yace bai damu don a kafa sabuwar Jam’iyya ba

– Dr. Bukola Saraki yace idan har tattalin arziki zai yi kyau, ta sa ta biya

– Bukola Saraki yace ya ajiye siyasa gefe guda, ya mayar da hankalin sa kan tattalin arziki

Ni ban damu dan a kafa sabuwar Jam’iyya ba Inji Saraki

Ni ban damu dan a kafa sabuwar Jam’iyya ba Inji Saraki

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki yace shi ba zai damu ba don a kafa wata sabuwar Jam’iyya in dai har tattalin arzikin Najeriya zai dawo daidai. Bukola Saraki ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da tashar Channels TV.

Bukola Saraki dai yace ya ajiye rigar siyasa gefe guda, yace babban burin sa shine ya ga tattalin arzikin Najeriya ya dawo daidai. Bukola Saraki kuma yake bayyana cewa Jam’iyyar su ta APC mai mulki tayi wasu kuskure a baya wanda yanzu an dauki darasi da su.

KU KARANTA: An kusa kashe wani don yace Buhari ya rasu

Ana dai yunkurin kafa wata sabuwar Jam’iyya a Kasar mai suna ADP. Kafuwar ADP din dai zai zama barazana ga Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar wanda tayi nasarar karbe shugabanci a hannun PDP shekaru biyu da suka wuce.

Shi dai Shugaban Sanatocin Kasar, Bukola yace bai damu ba don a kafa wata Jam’iyya a Kasar, yace abin da ke gaban sa shine shawo kan matsalar tattalin arzikin Kasar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel