SERAP ta rubutawa Buhari takarda kan zargin Babachir

SERAP ta rubutawa Buhari takarda kan zargin Babachir

- Kungiyar mai rajin tabbatar da gaskiya a sha'anin zamantakewar tattalin arziki SERAP ta ce, ya kamata shugaban kasa ya cire hannunsa daga kokarin hana gurfanar da Babachir a gaban kuliya

- SERAP ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya mika zargin cin hanci da a ke yiwa sakataren gwamantin tarayya David Babachir Lawal ga hukukomin da ke yakar cin hanci da rashawa

SERAP ta rubutawa Buhari takarda kan zargin Babachir

SERAP ta rubutawa Buhari takarda kan zargin Babachir

SERAP ta bukaci shugaban kasa da ya gaggauta mika zarge-zargen da a ke yi wa sakataren gwamantin tarayya Babachir David Lawal ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da kuma ICPC don zurfafa bincike, kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya in an same shi da laifi."

Kungiyar ta kuma ce Buhari ya gaggauta wallafa sakamakon binciken ta hannun Atoni janar kuma ministan sharia Abubakar Malami SAN, sannan ya sa Malamin ya mika fayal din ga EFCC da ICPC.

Mumuni ya ce:

"Mu na da damuwa cewa kasa dakatar da Mista Lawal daga matsayinsa na sakataren gwamnati har sai an gama bincike zai iya sa zargin da a ke na nuna son kai game da Lawal ya zama gaskiya."

Wasikar da a ka bawa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo kwafi ta ce:

"SERAP ta yi imani cewa turka-turkar mista Lawal za ta bawa gwamnatinku damar kara kwarin gwiwa ga 'yan Najeriya da dama da ka iya damuwa game da tambarinku na yaki da cin hanci da rashawa. A maimakon bada kariya ga lamarin, mu na ba ku shawara ku yi amfani da shi ku nuna wa 'yan Najeriya cewa ba za a samu adalci kala biyu ba yakar cin hanci da rashawa da gwamnatinku ke yi ba.

"SERAP ta kuma yi imani cewa shawarar za ta magance shakkun da jama'a ke yi ko gwamnatinku za ta iya magance cin hanci da ya yi katutu a cikin gwamnati.

"Ya na da matukar muhimmanci mutane su samu kwarin gwiwa da aminci a ikirarin gwamnatinku na yakar cin hanci da kuma kin hukunta ma su laifi"

"Gaskiya ne mista Lawal ya na da damar da tsarin mulki ya ba shi ta samun adalci wajen sharia wanda ya hada daukansa a matsayin wanda a ke zargi har sai kotu tabbatar da laifinsa.

"Amma wannan hakkin shi Lawal ne ya kamata ya magana a kansa ba gwamnatinku ba, musamman a matsayinsa na sakataren gwamnati.

''SERAP ta yi imani cewa, kotu ce kadai ke iya tantance Mista Lawal ba shi da laifi ta hanyar bin tsare-tsaren sharia."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel