Karancin man Fetur: Gwamnatin Jihar Sakkwato zata siyo litan mai 1m don jama’an jihar

Karancin man Fetur: Gwamnatin Jihar Sakkwato zata siyo litan mai 1m don jama’an jihar

Gwamnatin jihar Sakkwato ta kammala shirye shiryen sabunta yarjejeniyar cinikayya tsakanin tad a kamfanin man fetur na kasa (NNPC) don siyo litan mai miliyan daya da sayar da shi ga jama’an garin a duk sati.

Karancin man Fetur: Gwamnatin Jihar Sakkwato zata siyo litan mai 1m don jama’an jihar

Shugaban kwamitin tabbatar da samar da isashshen mai sakamakon karancin mai a jihar Alhaji Ibrahim Magaji ne ya bayyana haka yayin dayake jawabi dangane da aikin nasu.

Magaji yace, “nan bada dadewa ba, gwamnatin jihar zata siyo litan man fetur miliyan daya, kimanin tireloli 30 kenan.”

KU KARANTA:Baba Masaba ya mutu ya bar mata 130 da ýaýa 203

A cewar Magaji, wannan yunkuri ne da gwamnatin jihar tayi don samar da isashshen man fetur a jihar, don amfanin mutanen ta. Magaji ya bada tabbacin kwamitinsu zata tabbatar da samuwar man a duk fadin jihar.

“Zamu tabbatar da sa ido tare da tilasta bin dukkanin dokokin da suka shafi siyarwa da rabar da man fetur a jihar.” Inji Magaji

Daga karshe sai yayi kira ga yan kasuwannin da suka rufe gidajen man su da su gaggauta bude su, tare da siyar da man a kan kayyadajjen farashin gwamnati.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel