Uwargidar ministan shugaba Buhari ta rasu

Uwargidar ministan shugaba Buhari ta rasu

Mun samu labarin rasuwar mai dakin ministan matasa da wasanni Solomon Dalung, Brislika Dalung ta rasu.

Uwargidar Solomon Dalung ta rasu

Uwargidar Solomon Dalung ta rasu

Mataimaki na musamman ga minista Solomon Dalung, Genshak Gulak ne ya tabbatar ma kamfanin dillancin labaran (NAN) da rasuwar mai dakin ubangidan nasa.

KU KARANTA:Shugaban kasar Canada yayi tir da harin da aka kai ma musulmai a masallacin Quebec

Genshak ya shaida ma NAN cewar “Uwargida Briskila ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da gajeren rashin lafiya da tayi. ta rasu a wani asibiti mai zaman kansa a garin Jos.”

Uwargidar Solomon Dalung ta rasu

Uwargidar Solomon Dalung ta rasu

Wani wakilin NAN daya halarci gidan minista Solomon Dalung dake unguwar Sabon-Bariki, bai tarar da kowa ba sai illa maigadin gidan.

A can gidan marigayiya Briskila kuwa, jama’a ne ke ta kwarara, inda suke nuna alhininsu tare da yabawa da irin halin dattaku da mutunci irin na Briskila. Kafin rasuwar ta, Uwargida Briskila babbar jami’ar ce a hukumar kula da gidajen yari na kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Addu’a ne kadai zai iya kawo karshen ta’adanci a Najeriya - Yakubu Gowon

Addu’a ne kadai zai iya kawo karshen ta’adanci a Najeriya - Yakubu Gowon

Addu’a ne kadai zai iya kawo karshen ta’adanci a Najeriya - Yakubu Gowon
NAIJ.com
Mailfire view pixel