FUROFAGANDA: Za mu ta da yakin basasa idan Shugaba Buhari ya mutu

FUROFAGANDA: Za mu ta da yakin basasa idan Shugaba Buhari ya mutu

Wani matashi dan arewea ya wa ‘yan Najeriya baraza cewa idan jita-jita da ke yawo ya zama gaskiya shugaba buhari ya mutu, tooh fa! Sa a tayarda zauna tsaye.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari

Wani matashi dan arewea mai suna Haruna Maitala ya mayar da martani game da jita-jitan zargin rasuwar shugaba Muhammadu Buhari a shafin Fesbuk na sa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta amince a fitar da kudi Dala biliyan 1 da miliyan 200 don gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna

Haruna Maitala ya yi wannan gargadin ne a shafinsa ta Fesbuk, ya ce za a yi yakin basasa, idan wani abu ya faru da shugaba muhammadu Buhari.

Ya ce: "A cewa shugaba Buhari na cikin isashen lafiya da kuma jin dadin a Birtaniya, Allah de ya kiyaye, idan Buhari ya mutu Kiristoci da ‘yan kudancin kasar su sani cewa Osinbajo ko wani Kirista ba zai yi mulki ba saboda mulkin nan na ‘yan arewa ne. Ba zamu taba yarda a maimaita abinda ya faru a shekara 2010 ba.''

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 5 a inda suka bude wa wata masallaci wuta

Idan mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya ki ya yi murabus, tooh, ‘yan Najeraya su shira wa wata yakin basasa. Ko kuma Buratai ya yi juyin mulki. Ko a ranshar da wani daga arewa kuma Hausa Fulani, abin da muke so shine ya zama dan uwarmu ne a mulki. Wannan ya zama gargadi

A kwanan nan, wani fasto a Onitsha, Mmadukolu Christain Ejike, ya watsa wasu labarai a yanar gizo inda ya bukuci mutuwar shugaba Buhari. A cewar Fasto Ejike, Shugaba Buhari zai iya mutu kamar yada sauran tsohon shugabannin Najeriya suka mutu a karagar mulki kama Umaru Musa Yar'Adua, kuma Sani Abacha."

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel