Hukumar DSS ta tusa keyar Limamin cocin da yayi huduba a kashe Fulani

Hukumar DSS ta tusa keyar Limamin cocin da yayi huduba a kashe Fulani

– Kwanakin baya Fasto Johnson Sulaiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Makiyaya Fulani

– Yanzu haka Faston na shirin amsa gayyatar Hukumar DSS

– Faston ya nemi ayi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya

Hukumar DSS ta tusa keyar Limamin cocin da yayi huduba a kashe Fulani

Hukumar DSS ta tusa keyar Limamin cocin da yayi huduba a kashe Fulani

Babban Limamin cocin nan na Omega Fire, Fasto Johnson Sulaiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Fulani a duk inda suka ci karo da su kusa da cocin sa. Yanzu haka dai Hukumar DSS ta gayyaci Faston, ya kuma amsa gayyatar.

Limamin na cocin Omega Fire ya ba Mabiyan sa umarnin kashe duk wani Makiyayi da aka gani kusa da Cocin sa. Faston yake cewa a yanka masu wuya nan take, kuma babu abin da zai faru. Daga baya Faston ya jadadda cewa yana nan a kan bakan sa, sai dai yace bai da matsala da Hausawa ko Fulani masu neman zaman lafiya.

KU KARANTA: Domin karanta labaran mu sai a zamo tare da mu a nan

Hukumar DSS dai tayi kokarin kama wannan Fasto a baya, da wuri dai Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose yayi wuf ya ceci Faston. Daga baya Gwamnan yace akwai wani shiri na kama Faston daga Gwamnatin Tarayya.

Faston dai ya kira mabiyan sa da su guji yin zanga-zanga a dalilin kiran na sa da Hukumar DSS tay. Faston ya nemi mabiyan sa su cigaba da yi wa Najeriya addu’a. A yau ne dai Hukumar DSS za ta gana da Faston a dalilin kalaman sa na baya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel