Boko Haram sun kashe wani dalibin jami’ar Maiduguri

Boko Haram sun kashe wani dalibin jami’ar Maiduguri

Mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram sun hallaka wani matashi, kuma dalibi dan aji karshe a jami’ar Maiduguri mai suna Usman.

Boko Haram sun kashe wani dalibin jami’ar Maiduguri

Dalibi Usman

Dalibi Usman ya kammala jarabawarsa ta kammala ajin karshe a jami’ar Maiduguri kenan suka hallakashi yayin dayake kan hanyarsa ta komawa hutu gida. Abokansa da dama sun yi jimamin mutuwar Usman, inda suka tofa albarkacin bakunansu game da mamacin.

KU KARANTA:‘Yan Boko Haram sun kai hari barikin Soji, sun hallaka soji 3

Wani daga cikin abokan Usaman Goni M tar yace “yan Boko Haram sun kashe mana aboki yau a kan titin Biu, mutuwa rigace ga kowa, kuma muna matukar kaunar Usman, amma muna fatan Allah ya gafarta masa,ya saka shi a Aljanna Firdaus. Amin”

Shima wani abokin nasa, Lawan Alhaji Kyari yace:

“Inalilahi waina allaihir raju,un, ina sanar daku mutuwar abokin na Usman, wanda yan Boko Haram suka kashe shi a kan hanyar Biu, akan hanyarsa ta zuwa gida hutu bayan kammala jarabawarsa. Allahya jikansa da rahama.”

Muma a nan muna mika ta’aziyyar mu ga yan’uwa da abokan Usman, Allah yayi masa rahama, Amin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel