OFF sunyi rubutu ga shugaban kasa Buhari, sunyi barazanar tashin hankali

OFF sunyi rubutu ga shugaban kasa Buhari, sunyi barazanar tashin hankali

Kungiyar Oro Freedom Fighters (OFF) sun aika budaddiyar wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari suna gargadin cewa mayakansu da aka horar a Hong Kong zasu dawo Najeriya nan bada jimawa ba.

Kungiyar sunyi kira ga shugaban kasa Buhari da ya dauki tsarin da zai canja rayuwar mutanen yankin Niger Delta ta fanni mai kyau amma a sabon jawabi sun zarge shi da yin biris da tattaunawa.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta maida martani ga hana takardan izinin shiga Amurka ga yan Najeriya

A wata jawabi da hukumar NAIJ.com ta samu a ranar Litinin, 30 ga watan Janairu, kungiyar tace ta dade tana hakuri amma abun ya zama Kaman shugaban kasa bai shirya bin tsarinsu ba.

Tace bata damu da idan gwamnatain tarayya na horar sojoji don su fuskance su ba kamar yadda suma sun a shirye suke.

OFF sunyi rubutu ga shugaban kasa Buhari, sunyi barazanar tashin hankali

OFF sunyi rubutu ga shugaban kasa Buhari, sunyi barazanar tashin hankali

Karanta jawabin a kasa:

Kungiyar ta OFF ta gaji da hakuri a kan kin runguwar zaman lafiyarka a Najeriya. Ya kamata ka san cewa Najeriya ba kasar mutun daya bane, amma na kowa harma da wadanda ba’a Haifa ba. Gaskiya ne cewan idan ba’ayi halaka a Najeriya ba, bazaka nemi sulhu ba. Karda kayi addu’an halaka domin zai dauki rayukan masoyanka da dama.

Tun daga mulkin ka na soja zuwa na zabe, kana cewa zaka yaki cin hanci da rashawa da kuma rashin da’a alhalin akwai mutane da dama dake aikata hakan faraway daga kanka. Ba’a bada bayani kan kudin da aka kwato ba, kuma yan kasa na mutuwa a kan yunwa.

Ko da dai mutane da dama sunyi kamar basu san abunda ake ciki ba, amma kungiyar OFF bazata yi shiru ba. Ana tura masu gaskiya gidan yari amma ana rufe masu rashawa a ofishi. Ka dauka ko ka bari, mayakan OFF da aka horar a Hong Kong zasu dawo kasar Oro a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Bamu hana ka horar da sojoji ba, amma ka kwana da sanin cewa mata ne suka haifi sojoji. An baka kwanaki goma sha hudu ka sanar da jumhuriyar Niger Delta. Shugaban kasa, gani ga wane ya isa wane tsoron Allah.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel