Ko ta kaka sai mun mika Sanata Buruji Kashamu ga kasar Amurka - NDLEA

Ko ta kaka sai mun mika Sanata Buruji Kashamu ga kasar Amurka - NDLEA

- Hukumar kula da amfani da muggan kwayoyi wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA)tace ko ta kaka sai ta kai Sanata Kashamu kasar Amurka

- Ana zargin sanatan da shugabantan wata kungiyar yan kwaya a shekarun da suka gabata

Ko ta kaka sai mun mika Sanata Buruji Kashamu ga kasar Amurka - NDLEA

Ko ta kaka sai mun mika Sanata Buruji Kashamu ga kasar Amurka - NDLEA

Hukumar kula da amfani da muggan kwayoyi wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA)tace ko ta kaka sai ta kai Sanata Kashamu kasar Amurka

Hukumar tace: “Ya zama wajibi yanzu tunda wata kotun Amurka tace an fitar da sanatan zuwa kasar Amurka domin ya fuskanci ukuba."

KU KARANTA: Trump ya haramta shiga Amurka ka wasu kasashen musulmai

A ranan juma’a, 27 ga watan Junairu, wata kotun kasar Amurka ta yanke hukuncin cewa a fitar da sanatan zuwa kasar bayan tayi watsi da daukaka karan da yayi cewa kotu ta hana hukumar Amurka su kama sa akan laifin daukan kwayoyi.

Kashamu mai wakiltan mazabar Ogun ta gabas ya kasance shugaban wata kungiyar yan kwaya a shekaru da suka gabata a irnin Chicago, kasar Amurka.

Kana NDLEA ta bayyana cewa zata tabbatar da cewa duk wani umurni da zai hana a damke sanatan sai sunyi watsi da shi.

Game da cewar jaridan Punch, kakakin hukumar NDLEA, Mitchell Ofoyeju, ya bayyana a wata hira cewa NDLEA nada yarjejeniyar shari’a da kasar Amurka kuma sai ta zantar.

Yace: “Kun san wannan abu da ya faru yanzu hujja ne garemu akan wadanda suka bada umurnin cewa kada a kama shi.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel