Majalisar wakillai ta fara bincikar badakalar sansanin yan gudun hijira

Majalisar wakillai ta fara bincikar badakalar sansanin yan gudun hijira

Kwamitin dake kula da harkokin 'yan gudun hijira a karkashin shugabancin Sani Zoro ya ziyarci jihar Borno domin tattara bayanai akan kuskuren da sojojin mayakan saman Najeriya suka yi na kai harin bamabamai kan sansanin 'yan gudun hijira.

Majalisar wakillai ta fara bincikar badakalar sansanin yan gudun hijira

Majalisar wakillai ta fara bincikar badakalar sansanin yan gudun hijira

A karshen makon nan ne kwamitin ya isa jihar Borno inda mambobin kwamitin suka tattauna da gwamnatin jihar Borno da kungiyoyin kasa da kasa tare da wasu da suka samu raunuka sakamakon hatsarin.

Shugaban kwamitin Sani Zoro yace sun kawo ziyarar ce domin sanin musabbabin abun da ya haddasa kuskuren tare da tattara bayanan da zasu mikawa majalisar domin ganin irin matakin da za'a dauka da abubuwan da za'a yiwa mutanen da lamarin ya shafa.

Sani Zoro yace sun tambayi abun da ya faru kuma sun samu fahimtar abubuwan da suka gudana. Zasu rubuta rahoto su mikawa majalisar kamar yadda aka umurcesu.

Saidai Malam Sani Zoro yace yakamata gwamnatin tarayya ta soma tallafa wa 'yanuwan wadanda lamarin ya shafa. Ya kamata a biya diyya ga iyalan da 'yauwansu suka rasa rayukansu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau
NAIJ.com
Mailfire view pixel