Kiristoci a Arewa sun bukaci Buhari ya kama malaman addinai masu tunzura mutane

Kiristoci a Arewa sun bukaci Buhari ya kama malaman addinai masu tunzura mutane

Kungiyar Kiristoci ‘yan siyasa daga Shiyar Arewa sun yi kira ga gwamnatin Tarrayya da kakkausar Murya da ta dauki kwakwkwaran mataki akan shuwagabanin addini masu yin kalamai da ka iya tunzura al'uma.

Kiristoci a Arewa sun bukaci Buhari ya kama malaman addinai masu tunzura mutane

Kiristoci a Arewa sun bukaci Buhari ya kama malaman addinai masu tunzura mutane

Shugaban kungiyar Keftin E. Amuga wakilin Tangale, yace harkar zamantakewa zata shiga wani hali idan har gwamnatin Tarayya bata dauki matakin hana munanan kalamai da ka iya tunzura al’umma ba, inda yayi kira ga shugaba Mohammad Buhari ya hanzarta magance al’amarin.

Yace lokaci ya zo da yakamata mutanen Arewa su hada kansu tsakanin Kristoci da Musulmai a zauna lafiya, domin idan an sami zaman lafiya a Arewa to Najeriya zata sami zaman lafiya.

Itama wata jigo a kungiyar kuma mai hulda da mata a jihar Filato, Madam Christie Danfulani Sunkur, ta nemi ‘yan Arewa da su yi hakuri da juna Krista da Musulmi, ta hanyar hada kai da tsayawa kan tafarkin gaskiya ga juna.

Kungiyar ta ce tana karkata akalarta wajen taimakawa shugaba Buhari, inda suke tunkarar al’ummarsu da jawabai irin na jan hankali domin samun ci gaban Arewacin Najeriya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel