Manchester City na cikin babbar matsala saboda wannan dalilin (Karanta)

Manchester City na cikin babbar matsala saboda wannan dalilin (Karanta)

- Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta amince da tuhumar da hukumar kwallon kafa ta Burtaniya, FA, ta yi mata game da amfani da kwayoyin kara kuzari, bayan da ta kasa bayyana inda 'yan wasanta suka shiga ba a yi musu gwaji ba

- Ana dai bukatar duka kungiyoyin kwallon kafa su bayar da bayanai na gaskiya a kan atisayen da suke yi da kuma inda 'yan wasa suke a ko da yaushe domin a samu damar yi musu gwaji

Manchester City na cikin babbar matsala saboda wannan dalilin (Karanta)

Manchester City na cikin babbar matsala saboda wannan dalilin (Karanta)

Sai dai ana zargin City da rashin bayyana gaskiyar hakan har sau uku.

Hukumar dai na da wata doka wadda ta tanadi cin tarar duk wani kulob da ya gaza bayar da bayanan gaskiya sau uku.

An dai fahimci cewa kungiyar ba ta yi bayani game da sauye-sauyen da ta yi ba a kan horar da 'yan wasanta.

A wani labarin kuma, Real Madrid ta yi ban kwana da gasar Copa del Rey ta bana, bayan da Celta Vigo ta doke ta da ci 4-3 a karawa biyu da suka yi a wasannin daf da na kusa da na karshe.

A wasan farko da suka kara Celta ce ta ci Madrid 2-1 a Bernebeu, sannan kungiyoyin biyu suka tashi 2-2 a gidan Celta a ranar Laraba.

Celta ce ta fara cin kwallo bayan da Real ta ci gida ta hannun Danilo tun kafin a je hutu, kuma bayan da aka dawo ne daga hutun Madrid ta farke ta hannun Cristiano Ronaldo.

Daniel Wass ne ya ci Celta ta biyu kafin daga baya Lucas Vazquez ya farke wa Madrid.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel