APC ta Arewa-maso-yamma na taro a Katsina, ta yaba da salon mulkin Buhari

APC ta Arewa-maso-yamma na taro a Katsina, ta yaba da salon mulkin Buhari

- Shugabannin Jam'iyyar APC reshen Arewa maso Yammacin kasar nan, wato jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa, Sokoto, Kebbi da Zamfara, sun yaba gami da nuna gamsuwar su da salon shugabanci na shugaban kasa Muhammad Buhari

- Shugabannin Jam'iyyar sun bayyana hakan ne a yayin gagarumin taron da suka gabatar na Jam'iyyar APC shiyyar Arewa maso yamma wanda ya gudana a birnin Katsina

APC ta Arewa-maso-yamma na taro a Katsina, ta yaba da salon mulkin Buhari

APC ta Arewa-maso-yamma na taro a Katsina, ta yaba da salon mulkin Buhari

Mai magana da yawun shugabannin Jam'iyyar Shugaban Jam'iyyar APC na jihar Kaduna Alhaji Sadau Wada, ya kara da cewar, dukkanin alkawuran da Shugaban kasa Buhari yayiwa Jama'ar kasar nan ya cikasu, tun daga kan batun tabarbarewar tsaro daya addabi Kasar har ya zuwa batun inganta harkar noma, musanman a yankin Arewa maso yamma yankin da manoma suke kowa na fatan alkhairi da rokon Allah ya maimata mana.

Sadau Wada ya kuma kara da cewar a matsayinsu na 'ya'yan APC ya Zama wajibi suyi godiya ga Allah da kuma alfahari da shugabancin Shugaba Buhari, wanda duniya gaba daya ta shaida haka.

Shugabannin na APC reshen Arewa maso yamman sun kuma jinjinawa jagorancin shugaban Jam'iyyar reshen Arewa maso yamma Alhaji Inuwa Abdulkadir bisa ga kokarin da yakeyi wajen hada kawunan 'ya'yan Jam'iyyar a shiyyar, wanda kyakkyawan jagorancin nashi ne ya sanya APC a shiyyar Arewa maso Yammacin Kasar nan, ta zama babbar abar koyi ga sauran yankunan Kasar gaba daya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel