Fadar shugaban kasa ta maida martani ga hana takardan izinin shiga Amurka ga yan Najeriya

Fadar shugaban kasa ta maida martani ga hana takardan izinin shiga Amurka ga yan Najeriya

Bayan hukuncin da shugaban kasa Donald Trump ya gindaya a kan shige da fice, ana sanya ran cewa kasar Amurka zata daina ba yan Najeriya takardan izinin shiga na shekaru 2.

Fadar shugaban kasa ta maida martani ga hana takardan izinin shiga Amurka ga yan Najeriya

An shirya tsarin ne don kula da kasashen kamar yadda ake kula da Amurkawa ta fannin bayar da takardan izinin shiga. Najeriya na ba Amurkawa takardan izinin shiga na shekara daya ne kawai a halin yanzu yayinda a da Amurkawa ke ba Najeriya takardan izinin shiga na shekaru 2.

A cewar jaridar Vanguard, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, a gurin maida martani ga dakatar da takardan izinin shiga a ranar Lahadi, 29 ga watan Junairu, yace: “Wannan ba al’amarin fadar shugaban kasa bane”.

KU KARANTA KUMA: Karuwa ta shafa ma maza 500 cutar kanjamau a jihar Zamfara

Wani kididdiga da hukumar Naij.com tayi ya nuna cewa abun zai shafi yan Najeriya dake dauke da katin kasa guda biyu idan dayan fasfot dinsu ya kasance daga kasashen Syria, Iraqi, Iran, Sudan, Libya, Somalia da kuma Yemen, kasashen musulunci guda bakwai.

Ku tuna cewa bayan mako daya da rantsar da Trump a matsayin shugaban kasar Amurka, ya sanya hannu a kan wasu umurnin majalisa wanda suka hada da hana takardan izinin shiga ga mutanen Syria da wasu kasashen gabas ta tsakiya da kasashen Afrika.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel