Bayan hana musulmai shiga Amurka, sojan ta daya ya mutu

Bayan hana musulmai shiga Amurka, sojan ta daya ya mutu

- Rundunar sojin Amurka ta ce an kashe daya daga cikin sojojin kundunbalan ta sannan aka jikkata wasu uku, lokacin wani samame a shedkwatar kungiyar al-Qaeda a Yemen

- Shugaban Amurka Donald Trump ne da kansa ya bayar da umurnin kai samamen--wanda shi ne irinsa na farko tun bayan kama aikinsa

Bayan hana musulmai shiga Amurka, sojan ta daya ya mutu

Bayan hana musulmai shiga Amurka, sojan ta daya ya mutu

Daya daga cikin jiragen yakin Amurka da suka kai samamen ya yi mummunan sauka, abin da ya sa aka lalata shi a wurin dake lardin al-Baida.

Sojojin Amurkan sun ce sun kashe 'yan bindiga goma sha hudu.

Majiyoyi daga Yemen sun ce adadin wadanda aka kashe din ya haura sha hudu, sannan suka ce wasu gwamman fararen hula ma sun mutu.

Masu sharhi sun ce za a iya kallon samamen a matsayin irin hobbasa da sabon shugaban ya yi na daukan tsattsauran mataki akan kungiyoyin masu da'awar jihadi.

A wani labarin kuma, Iran ta ce za ta mayar da martanin da ya dace kan matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na hana Musulmi daga wasu kasashe 7 zuwa kasar.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce za ta hana daukacin Amurkawa zuwa kasar saboda abinda ta kira cin zarafin da Amurka ta yi wa ‘yan kasar ta, har sai Amurka ta sake matsayi akai.

Rahotanni sun ce an hana ‘yan kasar Iran da Iraqi hawa jiragen da ke tafiya Amurka saboda umarnin shugaba Trump.

Kamfanonin jiragen Etihad da Emirates da Turkish airline sun ce an umurce su da kar su sayar da tikitin Amurka ga ‘yan wadanan kasashe 7 ko kuma barin 'Yan kasar ta Iran da ke dauke da fasfo din Amurka hawa jirgin da zai kai su kasar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel