Kotu ta tsaida Donald Trump da manufar sa

Kotu ta tsaida Donald Trump da manufar sa

– Sabon Shugaban Kasar Amurka ya bada umarnin hana wasu baki shigowa Kasar Amurka

– Sai dai kuma Kotu ta dakatar da wannan shiri na Shugaban Kasar

– Yanzu haka dai wannan ya jawo hayaniya a Kasar Amurka

Kotu ta tsaida Donald Trump da manufar sa

Kotu ta tsaida Donald Trump da manufar sa

Kwanan nan, sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya saka hannu kan wata doka da ta hana baki shiga cikin Kasar Amurkar. Hakan dai ya sa aka tsare mutane da dama da suke kokarin shigowa a filin jirgi.

Wata Kotu da ke Brooklyn ce dai ta cece Jama’a, inda wani Alkali ya hana dabbaga wannan doka ta sabon shugaban Kasa Donald Trump. Wannan doka dai ta Donald Trump ta shafi har wadanda suke dauke da katin zama ‘Yan Kasar Amurka.

KU KARANTA: An kona wani Masallci a Amurka

A Ranar Juma’a Donald Trump dai ya nemi a hana bakin da ‘yan gudun hijira shigowa cikin Kasar na watanni hudu yayin da ya kuma haramtawa ‘Yan Kasar Siriya shigowa Amurkar har abada.

A wani harsashe da NAIJ.com tayi, an fahimci cewa ‘Yan Najeriya masu takardar shaidar zama ‘yan wata Kasar na iya fuskantar kalubale musamman idan dayar Kasar ta su tana cikin guda 7 da Trump ya hana shiga Amurka.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
NAIJ.com
Mailfire view pixel