Iran ta maidawa Amurka martani

Iran ta maidawa Amurka martani

– Sabon Shugaban Kasar Amurka ya bada umarnin hana wasu baki shigowa Kasar Amurka

– Sai dai Kasashen Duniya sun fara gayyatar wadanda Trump yake kora

– Ita kuma Iran ta haramtawa Amurkawa shiga Kasar ta

Iran ta maidawa Amurka martani

Iran ta maidawa Amurka martani

A Ranar Juma’ar nan, Shugaban Amurka Donald Trump ya nemi a hana baki da ‘yan gudun hijira shigowa cikin Kasar Amurka. Hakan dai ya sa aka tsare mutane kusan 200 da suke kokarin shigowa Kasar a filin jirgi kafin Kotu ta dakatar da shirin.

Sai dai Kasar Iran da ta shiga cikin sahun Kasashen da Trump ya hana shiga Amurka ba ta ji dadi ba. Kasar Iran ta mayar da martani inda tace za tayi wa Amurkar yadda tayi masu. Dama dai tun shekarar 1979 ba a shiri tsakanon Kasashen biyu.

KU KARANTA: Tirkashi: Ka ji abin da Trumo yayi?

Ministan harkokin waje na Kasar Iran ya soki tsarin na Trump yace ‘Yan ta’adda za su yi murna da hakan. Shugabannin Kasar Canada kuwa sun ce za su karbi bakin da aka hana shiga Amurka da hannu biyu.

Shugaba Trump dai ya hana Kasashe 6 shiga Amurka na watanni hudu yayin da ya kuma ya haramtawa ‘Yan Kasar Siriya shigowa Amurkar har abada. Wata Kotu da ke Brooklyn ce ta hana a dabbaga wannan doka ta sabon shugaban Kasa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel