Donald Trump zai dakatar da bizar 'Yan Najeriya?

Donald Trump zai dakatar da bizar 'Yan Najeriya?

– Sabon Shugaban Kasar Amurka na iya dakatar da bizar ‘Yan Najeriya

– Watakila dai Trump ya hana ‘Yan Najeriya shiga Amurka

– Tuni Trump ya dakatar da wasu kasashen 7 daga shiga amma Amurka; sai dai kuma fa…

Donald Trump zai dakatar da bizar 'Yan Najeriya?

Donald Trump zai dakatar da bizar 'Yan Najeriya?

Sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump na iya dakatar da bada takardun biza ga ‘Yan Najeriya wanda ke bada damar a zauna a Kasar Amurka har na shekaru biyu. Idan aka lura da abin da kyau, ana iya fahimtar cewa Najeriya na iya shiga cikin matsala.

A wani harsashe da NAIJ.com tayi, an fahimci cewa ‘Yan Najeriya masu takardar shaidar zama ‘yan wata Kasar na iya fuskantar kalubale musamman idan dayar Kasar ta su tana cikin guda 7 da Trump ya hana shiga Amurka.

KU KARANTA: Trump ya hana Musulmai shiga Amurka

Kasashen da Trump ya haramtawa shigowa Amurkar dai sune Siriya, Iraki, Iran, Somaliya, Libiya, Sudan da kuma Kasar Yemen. Sai dai kuma masu nazari sun bayyana cewa ba a tabu samun ‘Yan wannan Kasashen da ta’addanci a cikin Amurka ba tun fiye da shekaru 50 da suka wuce.

Najeriya dai tana ba 'Yan Amurka bizar shekara guda ne kurum a Kasar yayin da kuma ake ba ‘Yan Najeriya takardun zama na shekaru biyu. Ko ma dai ya abin yake, yanzu haka dai Kotu ta bada umarnin a dakatar da hana ‘Yan wasu Kasashen shiga cikin Amurkar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel