Boko Haram sun lalata coci-coci 900 - Kungiyar CAN

Boko Haram sun lalata coci-coci 900 - Kungiyar CAN

- Bangaren matasa na kungiyar kiristocin Najeriya ya ce sama da coci-coci guda 900 ne kungiyar Boko Haram ta tarwatsa tun farkon bullar ta

- Sun nemi gwamantin tarayya ta sake gina coci-cocin da a ka lalata sannan ta sake farfado da hukumar addinai wato Nigeria Inter Religion Council (NIREC)

- Ana sa rai kungiyar musulmai za su fitar da na su alkaluman dadadin masallatan da Boko Haram ta lalata

Boko Haram sun lalata coci-coci 900 - Kungiyar CAN

Boko Haram sun lalata coci-coci 900 - Kungiyar CAN

Bangaren matasa na kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta ce sama da coci-coci guda 900 ne kungiyar Boko Haram ta tarwatsa tun farkon bullar ta.

A cewarta coci-cocin da ke bukatar sake ginawa su na nan a jihohin Gombe da Yobe da Adamawa da Borno da sauransu.

Mayakan Boko Haram ne karkashin jagorancin Shekau ke da alhakin tashin bama-bamai da dama a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

kungiyar ta ci gaba da cewa, Coci-coci da ba su gaza 900 ba ne mayakan na Boko Haram su ka lalata tun farkon bullar kungiyar a Arewacin kasar, don suna kira ga gwamantin tarayya ta sake gina coci-cocin

Sun bayyana cewa cocinan da ke bukatar sake ginawa su na nan cikin jihohin Gombe da Yobe da Adamawa da Borno da sauransu.

Ana sa rai kungiyar musulmai za su fitar da na su alkaluman masallatan da 'yan Boko Haram ta lallata wadanda ake hasashen sun zarce yawan na kungiyar Kiristocin.

Domin a cewar masu lura da al'amura, duk da cewa Boko Haram na da'awar musulunci, amma ta ta fi kai hari kan masallatai fiye da coci-coci musamman a jihar Borno.

Domin ko a baya bayan nan, duk da cewa, sojoji na ikirarin ganin bayan kungiyar, 'yan ta'addan sun kai hari a masallacin Juma'a na jami'ar Maiduguri a inda suka lalata shi bayan kisan mutane da yawa ciki har da wani Farfesa.

Za ku iya bayyana ra'ayinku dangane da wannan labari a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http:www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel