Aregbesola ya yi tattaki zuwa Jamus

Aregbesola ya yi tattaki zuwa Jamus

- Gwamna Rauf Aregbesola ya jagoranci wata tawaga zuwa Kasar Jamus don nemo dabarun aikin gona na zamani wanda zai bawa jihar damar tabbatar da mafarkinta na zama cibiyar samar da abinci a kudu maso yamma

- Gwamnati ta yi imani cewa wannan zai taimaka wajen samar da aikin yi ga jama'ar mu ya kuma inganta rayuwar jama'ar jihar.

Aregbesola ya yi tattaki zuwa Jamus

Aregbesola ya yi tattaki zuwa Jamus

A ranar Asabar ne, tawagar da Ogbeni ke jagoranta ta sauka a Lindau a gundumar Anhalt Bitterfeld, a kasar Jamus kan batun aikin gona

Ogbeni Aregbesola ya yi wasu jerin tambayoyi game aikin gona na zamani, ya na mai fatan samun ilimi daga manoman kasar Jamus irin su Arnold de Vries wanda gwamnan ya ziyarta a gonarsa ta kiwon tumaki. Arnold de Vries ya dauki dalibai biyu daga jihar Osun don samun horo agonarsa a shekarar 2016.

Jihar Osun jiha ce ta noma kuma ta fi jihar Saxony-Anhalt girma amma a fagen noman zamani har yanzu ta na baya amma gwamnan da jama'ar sa a shirye su ke su kawo gyara.

Wannan ne ya sa a ka kaddamar da shirin "tallafawa harkar samar abinci " a shekarar 2012 tsakanin jihohin Saxony-Anhalt a Jamus da Osun a Najeriya, don matasan jihar su samu horo a dabarun aikin gona na zamani a jihar Saxony-Anhalt.

Sama da 'yan Najeriya 40 ne daga jihar Osun su ka amfana da wannan tsarin. Ogbeni Aregbesola ne ya tabbatar da haka yayin ziyarar da ya kai wa Bauer de Vries a Lindau.

"Mu na ciyar da al'ummar mu kuma kyakkyawan tsarin aikin gona kamar yadda a ke yi a nan Jamus zai taimaka mana." A cewarsa.

Ziyarar sa zuwa Saxony-Anhalt wata ziyara ce ta neman ilimi. Hakanan kuma an shirya tafiyar ne don godewa manoman da su ke ba da horo ga daliban da a ke kaiwa. Gwamnati ta zuba jari sosai a wajen kafa harsashin aikin gona na zamani a jihar kuma ta na sauraron girbi mai albarka.

In za iya tunawa kwanannan Ogbeni Aregbesola ya ba da umarnin dasa ayabar plantain guda miliyan 5 a jihar ta Osun don samar da abinci ga jama'ar jihar.

Gwamna Aregbesola ya samu rakiyar kakakin majalisar jihar Rt. Hon. Najeem Saleem da sakataren gwamnati Alhaji Moshood Adeoti da sauran jami'an manyan gwamanti.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016-
2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016- 2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel