APC ta bawa PDP kashi a zaben dan majalisar wakilai na jihar Edo

APC ta bawa PDP kashi a zaben dan majalisar wakilai na jihar Edo

- Jam'iyyar PDP a jihar Edo ta sha kaye a a hannun APC a wani zaben cike gurbin dan majalisar wakalai da aka gudanar

- An gudanar da zaben ne don cike gurbin tsohon wakili Philip Shuaib wanda ya zama mataimakin gwamnan jihar Edo

APC ta bawa PDP kashi a zaben dan majalisar wakilai na jihar Edo

APC ta bawa PDP kashi a zaben dan majalisar wakilai na jihar Edo

Jam'iyyar APC ta doke jam'iyyar PDP ne a zaben cike gurbi na dan majalisar wakilai na mazabar Etsako ta jihar Edo.

Zauren na majalisar wakilai da ake yiwa lakbi da 'Green Chamber' ya samu sabon mamba a jam'iyyar APC Johnson Oghuma wanda ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Etsako.

The Punch ta rawaito cewa Johnson Oghuma na jam'iyyar APC ya lashe zaben da kuri'u 39, 876 inda ya doke dan takarar jam'iyyar PDP Jude Imagwe wanda ya samu kuri'u 18, 193.

Kamar yadda baturen zaben, Farfesa Shola Omotola wanda ya bayyana sakamakon zaben da safiyar ranar Lahadi 29 ga watan Janairu kuma ya bayyana Oghuma a matsayin wanda ya lashe zaben, dan takarar APC ya yi nasara da kuri'u mafi rinjaye daga cikin kuri'u 59, 301 da a ka kada.

Duk da cewa guda 58, 427 ne karbabbu inda a ka ki karbar guda 874 bisa dalilai mabanbanta.

Oghuma ya amince da sakamakon zaben inda ya tabbatar wa da jama'ar mazabar cewa zai ma su wakilci yadda ya kamata. Ya ce:

"Ina tabbatar wa da jama'ar Etsako cewa ba zan ba su kunya ba. Zan ba su kyakkyawan wakilci kuma za a ji muryarsu kuma ba zan watsa ma su kasa a ido ba."

An gudanar da zaben ne don cike gurbin tsohon wakili Philip Shuaib wanda yanzu ya ke zaman mataimakin gwamnan jihar Edo.

ku cigaba da bin mu a sainmu na Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa ko a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel