Kiristoci ka iya kare kansu - In ji shuwagabannin katolika

Kiristoci ka iya kare kansu - In ji shuwagabannin katolika

- Kiristoci kan yi tunanin akwai shirye-shiryen cusgunawa wasu wajen gudanar da addininsu ta hanyar tashe-tashen hankula amma malamai sun fara magantuwa

- Biyu daga cikin manyan malaman cocin darikar katolika sun bi sahu wajen ci gaba da Allah wadai da a ke yi da rikice-rikicen addini a kasa

Kiristoci ka iya kare kansu - in ji shuwagabannin katolika

Kiristoci ka iya kare kansu - in ji shuwagabannin katolika

Biyu daga cikin manyan malaman cocin Roman Katolika sun bayyana cewa kiristoci na da 'yancin kare kansu yayin da a ka yi ma su barazana.

Babban shugaban na Jos kuma shugaban malaman darikar Cocin Katolika na Najeriya (CBCN), Babban Rabaran Ignatius Kaigama, da babban malamin Legas, Babban Rabaran Adewale Martins, sun magantu yayin da abin da a ke zargin ta'addanci ne ga kiristoci a arewacin Najeriya ke ci gaba da bazuwa.

Jaridar The Nigerian Tribute ta rawaito cewa, manyan malaman sun yi wannan bayani ne a bikin cikar Kungiyar 'Association of Sacred Heart of Jesus and Immaculate Heart of Mary, shekara 50 da a ka yi a cocin Agnes Catholic da ke Maryland a jihar Legas ranar Juma'a 27 ga watan Janairu.

A na zargin kashe kiristoci da dama a jihar Kaduna a hare-haren da a ka ce sai da su ka dauki watanni su na faruwa kafin hukmomi su dauki mataki.

A matsayarsa, Archbishop Kaigama cewa ya yi:

"Batun da ke cewa 'kashe su ko' ko ku rama' baya cikin koyarwar Annabi Isah. Addinin mu ba ya goyon bayan kisa.''

Amma hakan kuma ba ya nufin mu zauna mu zuba ido a na kashe mu da lalata dukiyoyinmu ba. Ku na da 'yancin kare kawunanku yayin da a ke ma ku barazana. Dokokin Ubangiji, da na mutane sun bayar da damar yin hakan.

Ba abu ne mai sauki ba zama kirista a wasu daga cikin wadannan jihohin na Arewa saboda haka dole ne mu hada karfi da al'ummar kirista wajen addu'a. Domin coci na cikin tashin hankali.

"An lalata duk wasu abubuwa da su ke hada kanmu amma ba za a iya lalata imaninmu ba. Idan mu ka rike Yesu hannu bibiyu." A cewarsa.

A bangarensa Archbishop Martins cewa ya yi:

"Duk wani dan adam na da 'yancin rayuwa da kare rayuwarsa yanda ta kamata. Don haka kiristoci da ma daukacin mutane na damar kare kansu yayin da su ke fuskantar barazana. Saboda haka abin da ya kamata mu yi ba fita za mu yi mu afkawa kowa ba. Domin ba a umarce mu da tashin hankali ba."

A 'yan kwanakin nan ne wani mai wa'azin Krista John Suleiman a jihar Ekiti ya yi kira ga mabiya addinin Krista da su dauki makamai su kuma farwa duk wani Fulani makiyayi da suka gani wanda hakan ya fusata jama'a, ya kuma Hukumar tsaro ta farin kaya ta shiga farautarsa.

Ku cugaba da bin mu a a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com/naijconhausa ko kuma a Tuwita a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel