Gwamnatin tarayya ta amince a fitar da kudi Dala biliyan 1 da miliyan 200 don gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna

Gwamnatin tarayya ta amince a fitar da kudi Dala biliyan 1 da miliyan 200 don gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna

- Gwamnatin tarayya ta amince a fitar da kudi Dala biliyan 1 da miliyan 200 don Gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna

- Ministan sufuri Rotimi Amaechi ne ya bayyana haka a yayin da ya kaiwa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ziyara

Gwamnatin tarayya ta amince a fitar da kudi Dala biliyan 1 da miliyan 200 don Gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna.

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ne ya bayyana haka a yayin da ya ke mika kyauta ga gwamna Abdullahi Ganduje a ziyarar da ya kai masa a ranar Asabar 28 ga watan Janairu.

Amaechi ya fadawa gwamna Ganduje cewa, gwamnatin tarayya na tattaunawa da bankin Exim na chana don daukar nauyin aikin.

"Mu na tattaunawa da bankin China Exim kuma mu na da nutsuwa tattaunawar za ta zo karshe a watan June." A cewarsa.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da na'urori sama da 100 da za su ratsa ta Legas da Kano da Fatakwal da Funtua da kuma Gombe don inganta tattalin arziki.

"Kafin karshen watan Jun layin dogo daga Kano zuwa Legas zai samu karin na'urori da za su ratsa ta Legas da Fatakwal da Kano da Funtua da kuma Gombe don bunkasa tattalin arziki."

Da ya ke mayar da jawabi, gwamna Ganduje ya bayyana jin dadinsa ya kuma yabawa shugaba Muhammadu Buhari wajen cika alkawarinsa na yakin neman zabe na gina layin dogo.

A cewar Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, gwamnan ya ce aikin zai ceto hanyoyin Najeriya daga durkushewa baki daya. Ya fadawa ministan cewa, kwanannan gwamntinsa ta sanya hannu a wata yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfanin kasar China don gina layin dogo a babban birnin jihar.

A cewarsa layin dogon zai mayar da Kano babban gari kamar wasu biranen da ke fadin duniya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel