YANZU-YANZU: Gobara a NNPC!

YANZU-YANZU: Gobara a NNPC!

Babban kamfanin man feturin Najeriya dake Suleja, jihar Neja ta kama da wuta da safiyan nan, Kamfanin dillancin labaran Najeriya wato News Agency of Nigeria (NAN) ta bada rahoto.

YANZU-YANZU: Gobara a NNPC!

YANZU-YANZU: Gobara a NNPC!

Shugaban kamfanin na jihar Neja Mr Mohammad Kwale,ya fadi wa NAN cewa a yau lahadi, wuta ta fara ci a defot din ne inda aka daukan man fetur.

Gobaran ta fara ne misalin karfe 4 :30 an dare sai aka kira mu. Misalin karfe 5 na safe, mun kashe wuta.

KU KARANTA: Soke-Soken da ake wa gwamnan jihar Kogi

''Wata mota ta kone kurmus kuma imda ake lodin man fetur da wasu bututu sun lalace. Amma dai ba’ayi rashin rai ba.

''Wani mazaunin garin Maje, Malam Garba Magaji, ya fadawa NAN cewa sunji wata kara wanda ya tashi mutane daga bacci a unguwan da safen nan, kari da cewa daga baya sukaji cewan daga NNPC ne.

”Karan fashewan tamkar na Bam. Amma wani abokin aikina ya fada mini cewa tayan wata motan mai lodin mai ne ya fashe.

”Yanzu dai an kulle wurin kuma ma’aikatan hukuma kashe wuta na wurin.” Wani yace

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel