Ba mu da aniyyar binciken lafiyar Buhari a Landan - NLC

Ba mu da aniyyar binciken lafiyar Buhari a Landan - NLC

- Kungiyar Kwadago ta kasa ta musanta zaragin da ake yi mata na kokarin bincikar lafiyar shugaba Buhari

- NLC ta ce ba ta da wata damuwa da lafiyar shugaba Buhari kuma ba kuma za ta bincika dalilin tafiyar sa hutu ba

Ba mu da aniyyar binciken lafiyar Buhari a Landan - NLC

Ba mu da aniyyar binciken lafiyar Buhari a Landan - NLC

A ranar 27 ga qatan Janairu Mista Ayuba Wabba wanda ke zaman shugaban kungiyar kwadagon, ya ce, kungiyar ba ta da sha'awar neman shugaba Buhari ya yi wa alummar kasa bayani kan yanayin lafiyarsa.

A cewar kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, mista Wabba ya ce, "Mu na so mu ji bayani a fili cewa ba mu taba yin wannan zance ba."

'Dalilin hakan ko a fili yake. A matsayin mu na kungiya ba ma aiki da jita-jita.

Abu na 2 mu na sane cewa, shugaban kasa ya na hutu kuma kafin ya tafi ya mika mulki ga mataimakin shugaban kasa.

"Mun kuma sani cewa, ikon shugaban kasa da rigar kariyarsa ba su hada da batun lafiya ba. Saboda haka kamar kowane irin dan adam, shugaban kasa ka iya yin rashin lafiya.

"Amma abu mafi muhimmanci a sha'anin lafiya da mutuwa na kowane dan kasa, ballantana ma na lamba 1, don haka 'yan kasa su na da muhimmancin da bai kamata a yi sako-sako da su ba

"Saboda haka mu na nisanta kanmu daga jita-jitar da a ke yadawa game da lafiyar shugaban kasa."

Wabba ya kuma gargadi kafafen yada labarai da su guji yada labaran da ba a tabbatar ba. Ya na mai cewa.

Yayin da mu ke shirin yi masa maraba idan ya dawo kasar, mu na kuma kira ga 'yan kasa kar su bari a jefa su cikin tsoro ta amfani da labaran kanzon kurege a kafafen yada labarai.

"Shugaba Buhari sai da ya cika duk wasu sharadai na barin ofis kafin ya tafi."

Haka nan kuma fadar shugaban kasa ta sanar cewa, za ta bincika ta kuma gurfanar da wadanda su ke yada jita-jita game da lafiyar shugaba Buhari.

Gwamnatin tarayya ta na bincika hanyoyin yada sakonnin zagon kasa ga gwamnati kan lafiyar shugaba Buhari.

Fadar shugaban kasa ta ce wadanda su ke cewa shugaba Buhari ya mutu za su gamu da fushin hukuma.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel