Jiragen da aka kwace na jihar Ribas ne - Wike

Jiragen da aka kwace na jihar Ribas ne - Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa jirage mau saukan angulu biyu da hukumar Kastam na Najeriya ta kwace na gwamnatin jihar Ribas ce kuma gwamnatin jihar ta rubuta wasika ta musamman ga shugaba Muhammadu Buhari domin kyautar da su ga hukumar sojin saman Najeriya.

Jiragen da aka kwace da jihar Ribas - Wike

Jiragen da aka kwace da jihar Ribas - Wike

Wike a wata jawabin da mai Magana da yawunsa , Simeon Nwakaudu, yayi a birnin fatakwal a jihar asabar,yace ya rubuta wasika ta musamman ga shugaban kasa saboda tsawallawan da hukumar kastam tayi akan jiragen da kuma kin gwamnatin tarayya da bari jiragen su wuce.

Yace: “Wadannan jiragen masu saukar angulu, gwamnatin da ta shude ne ta saye su; kuma lokacin da na shiga ofis, mun rubuta wasika ga gwamnatin tarayya cewa aikin tsaro kawai za’ayi amfani da su.

KU KARANTA: Adama Barrow ya canza sunan kasar Gambiya

“Na je gwamnatin tarayya ta bani takardan wucewa da su amma ta hana. Saboda haka, sai na rubuta wasika ga shugaba Buhari cewa wadannan jirage masu saukan angulun fa, aikin tsaro kawai za’ayi da su kuma za’a baiwa hukumar sojin saman Najeriya.

“ Munce ba zamu iya biyan kudin kastam din da akace mu biya ba saboda ba kasuwanci zamuyi da shi ba,amma domin bibitan yan baranda.

“A ina gwamnatin jihar Ribas zata samu kudi shigo da motoci bayan an saye su lokacin da akwai kudi a gwamnatin da ya shude.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel