Babu maganar karin farashin man fetur - IPMAN

Babu maganar karin farashin man fetur - IPMAN

– Masu jigilar mai sun tabbatar da cewa babu maganar kara farashin man fetur

– ‘Yan kasuwan sun ce babu wannan shiri a yanzu

– Kwanaki aka fara jitar-jitar watakila farashin fetur zai tashi

Babu maganar karin farashin man fetur-IPMAN

Babu maganar karin farashin man fetur-IPMAN

Kungiyar masu jigilar mai na Kasar nan ta bayyana cewa babu maganar karin farashin kudin man fetur. Kungiyar ta IPMAN na bangaren Kano tace Jama’a su daina daukar maganar cewa kudin mai zai daga.

Alhaji Bashir Dan Malam wanda shine Shugaban Kungiyar ta IPMAN a Kano yace za a kama duk wadanda suka sayar da mai a sama da farashin da Gwamnati ta saka. A Kano dai cikin ‘yan kwanakin nan mun samu labarin ana sayar da litan man fetur har a kan N155.

KU KARANTA: Tofa: An kai Najeriya Kotu

Dan Malam ya fadawa Hukumar Dillacin labarai cewa babu wani shiri na kara farashin man fetur din. Shugaban Kungiyar yace jita-jita ne kurum maras tushe. Dan Malam yace sun zauna da Gwamnati sun kuma shawo kan sabanin da suka samu na kudin don haka farashin mai na nan yadda aka sani.

Kwanaki NNPC dai suka ce man da su ke da shi a ajiye zai isa Najeriya har na fiye da wata guda. Matatar man Najeriya duk sun fara aiki don haka babu maganar a samu karancin kanaziri ko man babbar mota.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Hukumar zabe ta sanar da ranakun zaɓen fidda zakarun gwajin dafi na jam’iyyu

2019: Hukumar zabe ta sanar da ranakun zaɓen fidda zakarun gwajin dafi na jam’iyyu

An fara: INEC ta kaɗa gangan siyasar 2019, ta sanya ranakun gudanar da zaɓen fidda yan takara
NAIJ.com
Mailfire view pixel