EFCC ta taso keyar tsohon Gwamnan Adamawa

EFCC ta taso keyar tsohon Gwamnan Adamawa

– Hukumar EFCC tana zargin tsohon gwamnan jihar Adamawa, Umar Fintiti da karkatar da wasu kudi

– Ana zargin Fintiri da yin sama da kusan Naira Biliyan uku lokacin da ya rike gwamna

– Ana nan ana buga shari’a a wani Babban Kotu da ke Abuja

EFCC ta taso keyar tsohon Gwamnan Adamawa

EFCC ta taso keyar tsohon Gwamnan Adamawa

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa tana zargin Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da karkatar da wasu Naira Biliyan 2.8. Yanzu haka dai ana ta shari’a a babban Kotun Tarayya da ke Maitama a Abuja.

Kamar yadda Jaridar Vanguard tace yanzu haka dai har Hukumar EFCC ta fara kiran shaidun ta domin su yi magana a gaban Kotun. Yanzu haka dai an daga karar zuwa 2 ga watan Maris domin cigaba da shari’a.

KU KARANTA: Ku taya Shugaba Buhari da addu'a

Fintiri ya kasance tsohon Kakakin Majalisar Jihar ta Adamawa, ya kuma rike Gwamnan Jihar ne na wani dan lokaci bayan an tsige Gwamna Nyako. Daga baya kuma Kotu ta maida tsohon Mataimaki, James Bala Ngillari a matsayin Gwamna.

Haka kuma ana zargin Tsohon Gwamna, Murtala Nyako da karkatar da wasu kudi har Naira Biliyan 40 a lokacin yana Gwamna. To sai dai yanzu an samu cikas a wajen shari’ar Tsohon Gwamnan har kuma an dage karar sai wata mai zuwa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel