Ban yi nadama ba, inji faston da yace a kashe Fulani

Ban yi nadama ba, inji faston da yace a kashe Fulani

– Fasto Johnson Sulaiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Makiyaya Fulani kwanakin baya

– Faston yace duk Makiyayin Fulani da aka gani kusa da Cocin sa a aika sa lahira

– Har yanzu dai yace ba zai nemi gafarar abin da ya fada ba

Ban yi nadama ba, Inji Faston da yace a kashe Fulani

Ban yi nadama ba, Inji Faston da yace a kashe Fulani

Fasto Johnson Sulaiman na cocin na Omega Fire ya ba Mabiyan sa umarnin kashe duk wani Makiyayi da aka gani kusa da Cocin sa. Faston yace a yanka masu wuya nan take, sai dai wadannan kalamai sun nemi su tada Kasar.

Faston yace ba zai nemi gafarar kowa ba, Faston ya fadi haka ne a wata huduba da yayi wa Mabiyan na sa. Faston dai yace ba fada yake da Fulani ko Hausawa ba, ya kira su mutanen kirki masu hakuri.

KU KARANTA: Gwamna ya zama Direban Fasto

Shi dai Faston yace idan har aka ga wani Bafullatani ya shigo cikin cocin na sa ko da wasa ne a aika sa lahira. Faston yace don kuwa Fulani suna kashe Kiristoci a fadin Kasar babu abin da kuma aka yi, don haka su ma za su yi hakan.

Hukumar DSS dai ta nemi ta cafke Fasto Sulaiman bayan yayi wannan kalamai, Gwamna Fayose na Ekiti yayi wuf ya je ya hana. Tun bayan nan ne kuma Gwamna Fayose ya zama Direban Faston.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel