Tashin hankali: Ka ji kudin da wani gwamna ya handame cikin shekara guda?

Tashin hankali: Ka ji kudin da wani gwamna ya handame cikin shekara guda?

– ‘Yan Jam’iyyar APC sun hurowa Gwamna Yahaya Bello wuta

– Ana zargin Yahaya Bello da yin sama da makudan Biliyoyin kudin Jihar

– Sanata Melaye da sauran wasu ‘ya ‘yan Jam’iyyar sun tasa Gwamnan a gaba

Tashin hankali: Ka ji kudin da wani Gwamna ya handame cikin shekara guda?

Tashin hankali: Ka ji kudin da wani Gwamna ya handame cikin shekara guda?

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi dai ya shiga halin ni-’ya su bayan Jam’iyyar su ta APC ta kara huro masa wani sabon wuta inda ake zargin sa da yin sama da fiye da Naira Biliyan 230 cikin shekara guda da yayi yana mulki.

Jam’iyyar ta ba Gwamnan makonni hudu cur da ya biya tsofaffin Ma’aikatan Jihar kudin sun a fansho wanda yana nan a ajiye kamar yadda suka fada. Jam’iyyar dai ta zargi Gwamnan da kashe kudi sama da Biliyan 200 daga hawan sa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kusa dawowa

Sanata Dino Melaye dai yana cikin wadanda suka hallarci wannan taro, sannan kuma akwai Shugaban Jam’iyyar na Jiha Haddy A. Ametuo da kuma da yawa daga cikin shugabannin Jam’iyyar. Dino Melaye dai yace yayi da-na-sanin hawan Gwamnan da ya kira ‘dan-bera’

Kwanan nan wasu Tsageru daga Yankin Agatu suka sace wani Sarki na Hausawa a Jihar Kogin yayin da ya ke ta sharar barci cikin dare. Wannan abu dai ya faru ne a Yankin Bagana da ke cikin Karamar Hukumar Omala a Jihar Kogi.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel