Jami'an shige da ficen Amurka sun fara hana musulmi shiga kasar

Jami'an shige da ficen Amurka sun fara hana musulmi shiga kasar

- Biyo bayan umarnin hukmomi na hana musulmai daga kasashen musulmi guda 7 shiga Amurka, rahotanni sun nuna a na tare musulman da ke balaguro a kan iyaka

- Amurkawa da dama irin su Mark Zuckerberg sun soki lamirin umarnin korar muslmai 'yan cirani daga Amurka

Jami'an shige da ficen Amurka sun fara hana musulmi shiga kasar

Jami'an shige da ficen Amurka sun fara hana musulmi shiga kasar

Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin rufe kan iyakokin Amurka ga 'yan gudun hijira na tsahon wata 4.

Bugu da kari an hana masu balaguro daga kasashen musulmi 6 shiga kasar ba tare da la'akari da ko an ba su izinin zama a kasar ba ko 'a a

A cewar kafar labarai ta The Telegraph, yayin da ya ke sanya hannu a umarnin, shugaba Trump ya ce:

"Muna so mu tabbatar cewa ba mu shigo da wadanda barazana ce ga sojojinmu ba.

"Mu na so mu shigo da wadanda za su goyi bayan kasarmu, su kuma kaunaci mutanen mu sosai."

Trump dai ya sha suka daga shahararrun Amurkawa ciki har da mamallakin Facebook, Mark Zuckerberg, game da umarnin da ya bayar na hana musulmi shiga Amurka.

An rawaito cewa, a na dawo da matafiya da a ka bawa izinin shiga kasar, ko kuma a ce ma su kar su hau jirgi saboda hanin da a a ka yi.

Muhammed Alrawi, wanda ya kammala karatu a jami'ar jihar California kuma tsohon dan jarida da ya yi aiki da The Los Angeles Times ya ce, an canjawa mahaifinsa wurin zuwa ta karfi a Qatar sanadiyyar hunkuncin na mista Trump.

Alrawi ya rubuta a Facebook cewa:

"Mahaifina dan shekara 71 ya na Qatar inda ya hau jirgin LAX don ya kawo mana ziyara amma a ka mayar da shi Iraq. Wasu jami'an Amurka su ka shaida ma sa cewa Trump ya soke izinin shiga kasar."

Wanda ya kirkiro Facebook, Mark Zuckerberg ya ce, a wani rubutu da ya yi, na cewa, ya damu a kan tasirin da umarnin zai yi, sannan zai yi aiki da Fwd US, wata gidauniya da ya ke kula da ita don bayar da kariya ga yara 'yan cirani da iyayensu su kawo su Amurka. Zuckerberg ya rubuta a Facebook:

"Kakanni na sun zo daga Germany da Austria da kuma Poland. Iyayen Priscilla 'yan gudun hijira ne daga China da Vietnam. Kasar Amurka kasa ce ta 'yan cirani kuma ya kamata mu yi alfahari da hakan.

"Kamar da yawa daga cikin ku, na damu da tasirin da hunkuncin da shugaba Trump ya dauka. mu na bukatar mu tsare wannan kasa, amma ba ta hanyar mayar da hankali kadai kan wadanda su ke barazana ba.

"Fadada akalar doka fiye wadanda a ke ganin su ne barazana, zai sa Amurkawa su samu karancin tsaro ta hanyar karkatar da dukiya, yayin da miliyoyin mutanen da ba sa ba da waccan barazanar za su kasance cikin dar dar.

''Dole kuma mu bar kofofinmu a bude ga 'yan gudun hijira da masu neman taimako. Da mun kori 'yan gudun hijira shekaru 10 da suka wuce, da iyalan Priscilla ba su kasance a nan ba."

Haka kuma tsohon sakataren cikin gida na Amurka, Madeleine Albright, ya ci alwashin zama musulmi in har Trump zai hana musulmi shigowa kasar.

Albright wadda ita ce sakarariyar Harkokin cikin gida mace ta farko karkashin mulkin Bill Clinton, ta rubuta a tweeter ranar Laraba 26 ga watan Janairu cewa:

"Na taso a 'yar darikar katolika na zama Episcopalian kuma daga baya na gano 'yan uwana yahudawa ne."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel