Sarki Sanusi ya gargadi malamai da su daina wa'azin nuna kyama

Sarki Sanusi ya gargadi malamai da su daina wa'azin nuna kyama

- Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na 11 ya gargadi malaman addinai da su iya bakinsu, hakan ya biyo bayan rikicin da ya ki ci yaki cinyewa a kudancin Kaduna

- Sarkin yayi wannan kira gami da gargadin ne a yayin bude wani masallacin Juma'a jihar Naija

Sarki Sanusi ya gargadi malamai da su daina wa'azin nuna kyama

Sarki Sanusi ya gargadi malamai da su daina wa'azin nuna kyama

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya ja kunnen malaman addinai da su iya bakinsu tare da daina furucin da ke koyar da kyama.

Wannan shawarar ta Mai martaba Sarki ta biyo bayan tashin hankalin da ke faruwa a wasu sassan kasar nan ciki har da kudancin Kaduna.

Yayin da wasu ke danganta tashin hankalin da Fulani makiyaya da mazauna wurin, wasu na ganin rikicin addini ne.

Bayan nasiha kan wanzar da zaman lafiya, sarkin ya bukaci malaman musuluncin da su yi aiki don zama lafiya da mabiya wasu addinan. A cewarsa wa'azin kyama ya sabawa addinin musulunci.

The Punch ta rawaito cewa, sarkin ya fadi haka ne a wajen bude wani masallaci na zamani a jami'ar fasaha ta gwamantin tarayya da ke Minna jihar Niger ranar Juma'a 28 ga watan Janairu 2017.

Mai martaba Sarkin ya kuma nuna bacin ransa game da yadda wasu malamai ke amfani da damar su ta tada rikici tsakanin al'umma.

Mai marataba sarkin ya kuma ce: "Ya kamata malamai da sauran musulmi su yada zaman lafiya a cikin mabiya kuma su yi aiki don cimma zaman lafiya da mabiya wasu addinan."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel