Budurwar gwamna ta tsere da Dala Miliyan 10

Budurwar gwamna ta tsere da Dala Miliyan 10

- Budurwar wani gwamna na daya daga jihohin kudancin kasar nan, ta tsere da Dalar Amurka Miliyan 10 na kudin biyan ma'aikata daga gwamnatin tarayya da ya boye a wurinta

- Gwamnan wanda ya ke daga daya daga cikin jihohin da ke da arzikin man fetir ya fada komar EFCC a inda ta soma binciken yadda aka haihu a ragaya

Budurwar gwamna ta tsere da Dala Miliyan 10

Budurwar gwamna ta tsere da Dala Miliyan 10

Hukumar EFCC ta dukufa wajen gano yadda wani gwamna na yankin kudu masu kudu mai arzikin mai ya karkatar da Dalar Amurka miliyan 10 da gwamnatin tarayya ta bayar na biyan ma'aikata albashi kuma farkarsa ta gudu da su.

Jaridar ta The Nation ta bayar ta rahoton cewa, gwamnan ya ba budurwar ta sa kudin ne, domin ta sarrafasu su zama na halal, amma sai zakara ya ba ta sa a, domin ta ki ta sa ko kwabo a asusun ajiyar banki na bayan fagen da ya ba ta.

KU KARANTA KUMA: Zaharaddeen Sani ya musanta zargin neman maza

A bibiyar kudin an ganosu a wani banki a Amurka, kuma wani sakamakon bincike da jaridar ta yi ta ce, gwamnan ya boye kudin ne a wurin budurwarsa domin gujewa binciken jami'an tsaro.

Sai dai daga karshe an gano cewa, an fitar da kudin ne ta hanyar aikawa da su ta hanyar wannan asusun ajiyar banki zauwa wancan a cure, ko kuma a tsit-tsinke domin batar da sahu daga jami'an tsaro masu sa ido.

Daya daga cikin wadanda ke aikin binciken ya ce, gwamnan wanda bai bayyana sunansa ba, daga dukkan alamu budursa wacce ke zaune a jihar Texas a Amurka ta damfare shi gwamnan wadannan kudin da ya sata ne, shi bai sani ba.

Kudin na daga cikin kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar domin biyan ma'aikatan da jihar ta kasa biyansu albashi, amma ya sace ya kuma ba budurwar tasa domin a juya masa ya samu riba, amma sai sata ta saci sata.

Jami'in tsaron ya kuma ce, nan ba da dadewa ba za a bayyana sakamakon binciken

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta bayyana cewa jihohi 16 ne suka karkatar da kudaden da aka ba su rance domin biyan ma'aikatansu albashi da suka gaza biya.

Aiko da ra'ayinka dangane da wannan labari a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com/naicomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel