Gwamna ya koma dogarin Fasto a Ekiti

Gwamna ya koma dogarin Fasto a Ekiti

Gwamna Fayose ya koma zagi kuma direban Fasto John Suleiman wanda ya yi katobarar kiran mabiyansa da yin kisa

Gwamnan ya yi hakan ne a kokarin sa na kare faston daga kamun da Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ke kokarin yi a bisa furuncinsa daka iya haddasa rikicin addini a kasa

Gwamna ya koma dogarin Fasto a Ekiti

Fasto John Suleiman da jami'an hukumar DSS a na kulli kurciya da taimakon Fayose

A kokarinsa na kare wani mai wa'azin addinin kirista John Suleiman daga shiga hannun Jami'an tsaro na farin kaya DSS, gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya koma yi masa zagi

Gwamnan wanda ba ya rabo da ce-ce-ku-ce, ya hana Jami'an Hukumar DSS kama mai wa'azin Kiristan ne bayan wani zuga mabiya addinin Kirista da ya yi na su kashe Fulani Makiyaya.

Duk da cewa Fasto John ya musanta cewa ya zuga mabiyansa duk da hotunan bidiyon na furuncin sa da aka yi ta yadawa na haddasa yaki mai nasaba da addini, ya amsa cewa shi dai kira ya yi da su kare kansu, amma hakan bai sa Hukumar DSS ta hakura ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Buhari ba zai iya magance matsalar Najeriya ba – Balarabe Musa yayi magana

A wasu jerin hotuna na gwamnan da ake yadawa an ga gwamnan na yiwa Faston mai katobara zagi tare ba shi kariya na kar a kama shi, hatta a wurin da ya ke gudanar da ibada an ga gwamnan shi ma a durkushe yana yi wa Najeriya addu'a.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da gwamna Fayose na jam'iyyar PDP ya hana jami'an hukumar gwamnatin tarayya gudanar da aiki su a jihar ba.

Domin a kwanakin baya gwamnan ya hana jami'an EFCC hana kama matar Fani-Kayode don yi mata tambayoyi yayin da ta je cire wasu kudi a wani asusun ajiyar banki da hukumar ta hana a taba sakamakon bincike da ta ke yi a kai.

Haka ma a jihar Rivers gwamna Nyesom Wike na Jam'iyyar PDP ya hana jami'an hukumar DSS kama wani mai shari'a da ake zargi da cin hanci da rashawa a shekarar da ta wuce

Wannan sabon salo na adawar siyasa na hana jami'an tsaro gudanar aikinsu a jihohin da gwamnonin PDP ke mulki tuni ya janyo ka-na-ce a shafukan sada zumnta da muhawara na intanet.

A inda mutane da yawa ke ganin beken gwamnonin da kuma zarginsu da wuce gona da iri na amfanin da rigar kariyar da kundin tsarin mulki ya ba su.

Ku ci gaba da bin mu a shafinmu na Facebook a http://facebook.com/naijconhausa da kuka a Tuwita a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel