Imam ya bukaci yan Najeriya da suyi ma Buhari addu’a

Imam ya bukaci yan Najeriya da suyi ma Buhari addu’a

Jita-jitan mutuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wani malamin musulinci Sheik Sule Atigo ya yi kira gay an Najeriya da suyi ma shugaban kasa addu’a.

Tun bayan tafiyarsa hutu birnin Landan, an samu jita-jita cewa shugaban kasar baida lafiya duk da dai fadar shugaban kasa ta karyata hakan.

Imam ya bukaci yan Najeriya da suyi ma Buhari addu’a

Imam ya bukaci yan Najeriya da suyi ma Buhari addu’a

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa babban liliman na masallacin juma’an Unguwar Gwari yayi magana a ranar Juma’a 27 ga watan Junairu a lokacin sallar Juma’a inda ya bukaci Yan Najeriya da su koyi halin yiwa shugabanninsu addu’a.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na zagi shugaba Buhari, Sanata Shehu Sani yayi magana

Yace: “Yan Najeriya su koyi dabi’ar yiwa shugabanninsu addu’an kariyar Allah gurin tabbatar da gwamnatin damokradiya mai kyau.

“Yan Najeriya su guje ma sharhi daga jita-jita sannan kuma suyi ma shugaban kasa addu’a.

“Ubangiji na da dalilin samar damu daga kabilu, yare da kuma addini daban-daban.

“Dole mu jurewa zama da juna don zaman lafiya, ci gaba da kuma dorewar siyasar kasar mu."

Ya bukaci yan Najeriya da suci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya ta hanyar basu bayanai da zai kai ga kama masu laifi.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel