Donald Trump yayi wata katabora

Donald Trump yayi wata katabora

– Sabon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya buga wata katabora

– Theresa May ta ziyarci Shugaba Donald Trump

– Firayim Minista May ta gargadi Trump ya bi a hankali da Kasar Russia

Donald Trump yayi wata katabora

Donald Trump yayi wata katabora

Sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya buga wata katabora yayin da Firayim Ministan Birtaniya, Theresa May ta kai masa ziyara. Donald Trump ya kira Theresa May ta Birtaniya da suna Teresa May.

Teresa May dai shahararriyar ‘Yar wasan fina-finan banza ce. Firayim Ministan Kasar Birtaniya Theresa May ta kai ziyara ne ga Shugaban Kasa Donald Trump na Amurka. Mako guda kenan da hawan Donald Trump mulkin Kasar Amurka.

KU KARANTA: Amurka tana da labarin za a tsige Buhari

Kamar yadda aka sani sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya sha alwashin kare iyakokin Kasar Amurka daga bakin haure. Yanzu haka Trump ya bada umarnin a fara shirin gina katuwar katanga tsakanin Kasar Amurka da Kasar Mexico masu makwabtaka da juna.

Theresa May ce dai farkon wanda ta fara ziyartar Donald Trump. May ta gargadi Trump ya bi a hankali da Kasar Russia a ganawar su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel