Ku bi tafarkin Fayose - Godswill Akpabio ga gwamnonin PDP

Ku bi tafarkin Fayose - Godswill Akpabio ga gwamnonin PDP

Shugaban maras rinjayen majalisar dattawa, Godswill Akpabio,yayi kira ga gwamnonin jam’iyyar PDP cewa su yi koyi da gwamnan jihar Ekiti,Ayodele Fayose.

Ku bi tafarkin Fayose- Godswill Akpabio ga Gwamnonin PDP

Ku bi tafarkin Fayose- Godswill Akpabio ga Gwamnonin PDP

Godswill Akpabio,yayinda yake Magana a taron gangamin shugabannin jam’iyyar PDP da akayi a ranan Alhamis,26 ga watan Junairu a Abuja, ya jinjinawa Fayose akan maganganun da yakeyi.

Tsohon gwamnan Akwa Ibom yace wasu sanatoci daga jam’iyyar APC sun yanke shawaran dawowa PDP idan aka kwantar da kuran da ke cikin PDP.

Yace duk da cewa mambobi sun sheke jam’iyyar APC, har yanzu sunada mambobi da dan dama a majalisar dokoki.

KU KARANTA: TInubu ya jaddada goyon bayansa ga Buhari

Yace: “Babu zaben da za’a sake yi a jihohin PDP 28 da jam’iyyar ba zata ci ba yanzu. Yanzu da nike muku magana, akwai sanatoci da dama masu son dawowa jam’iyyar PDP. Abunda suke jira kawai shine an kwantar da kuran da ke cikin jam’iyyar idan akayi haka,ina tabbatar muku da cewa sanatoci 20 zasu dawo PDP.

“Wannan sako ne ga wadanda ke kokarin shekewa APC saboda PDP zata dawo kan diga-digenta a shekarar 2019."

Godswill Akpabio, ya nuna bacin ransa akan fadi zaben da jam’iyyar tayi a jihohin Edo da Ondo, tayi kira da jam’iyyar su hada kansu kafin zuwan zaben jihar Anambra da Ekiti.

https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel