Ministan shari’a ya bayyana yadda gwamnati ta kwato makudan kudi daga hannun barayin

Ministan shari’a ya bayyana yadda gwamnati ta kwato makudan kudi daga hannun barayin

Zuwa yanzu gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kwato makudan kudi daga hannun barayin jami’an gwamnati da suka hada da naira biliyan 15, da dalan Amurka miliyan 10.5, inji ministan shari’a na kasa Abubakar Malami.

Ministan shari’a ya bayyana yadda gwamnati ta kwato makudan kudi daga hannun barayin

Ministan shari’a Abubakar Malami

Malami ya bayyana haka ne a yayin dayake jawabi lokacin da yan kwamitin majalisar dattawa dake kula da bangaren shari’a da kare hakkin bil adama, inda Malami ya bayyana musu manyan manufofin gwamnatin nasa.

Malami ya bayyana manufofin gwamnati guda hudu kamar haka: Yaki da cin hanci da rashawa, kwato kudaden gwamnati daga hannun baragurbin jami’an gwamnati da yan kwangila, tabbatar da bin doka ka’ida, yaki da ta’addanci sai kuma habbaka tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA:Halin matsin tattalin arziki: Gwamnatin tarayya zata ƙara ma ma’aikata albashi

Ministan yace kudaden da ma’aikatar shari’a ta nema don yin aikace aikacenta naira miliyan 405, 540, 000, amma kudaden data kashe ya kai naira biliyan 3, 672, 730, 661.

Shima shugaban kwmaitin Sanat David Umoru yace kasafin kudin shekarar 2016 ya sha fama da tasgaro daban daban yayin da ake shirya shi, amma ya tabbatar da cewa zasu yi kokarin ganin sun tabbatar da kasafin kudin bana akan lokaci.

Hakazalika shugaban kwamitin yaki da cin hanci na majalisar dattawa Sanata Utazi Chukwuka yace har yanzu kasar Najeriya bata samu shiga kungiyar kwato kadarorin gwamnati na duniya dake kasar Faransa ba, inda yace gwamnatocin baya sunyi kokarin mika takardun nuna sha’awa ne kawai.

Amma ya jinjina ma gwamnatin tarayya na yadda ta kwato makudan kudade daga hannun barayin gwamnati kimaminin naira miliyan 12, sai dai ya koka da kin amsa kira ministan ya ki yi yayin da suka gayyace shi, musamman a lokacin da aka kai ma wasu alkalan kotun koli hari.

Amma minista Malami bai bari ta huce ba yayi wuf ya nemi afuwar ya majalisar saboda rashin smaun daman amsa gayyatar da suka yi masa, inda yace bai samu takardan sammacin ba, sa’annan ya kara da cewa amma ai ya gurfana gaban kwamitin na majalisar wakila a lokacin daya samu takardan gayyata.

Game da shiga kungiyar Faransa kuwa, ministan yace ai rashin sahhale dokar ne da majalisun dokokin nan basu yi ba ne ya kawo tsaikon Najeriya kasancewa daya daga cikin yayan wannan kungiyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel